A cikin shirin za a ji cewar jagororin zanga-zangar da ta yi sanadiyyar faduwar gwmanatin tsohon Shugaba Umar al-Bashir a Sudan sun bukaci a rusa majalisar mulkin sojin don maye gurbinta da ta farar hula cikin gaggawa, yayin da Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi barazanar dakatar da Sudan daga cikinta idan sojoji basu mayar da kasar ga mulkin farar hula ba.