Cikin shirin za a ji cewa Emmerson Mnangagwa wanda ake shirin rantsarwa a matsayin sabon shugaban kasar Zimbabuwe na riko ya isa kasar daga Afrika ta Kudu a wannan Laraba, a karon farko da ake ganin shi a bainar jama'a tun bayan rikita-rikitar da ta tilasta masa barin kasar.