A cikin shirin za a ji cecekucen da ake yi kan wani atisaye da sojojin Najeriya ke yi a jihohi biyar na al'ummar Igbo tare da yin kashedi ga 'yan haramtacciyar kungiyar Biafra a yankin. 'Yan Afirka ta Kudu sun soki kalaman Shugaban Amirka Donald Trump kan dokokin mallakar filaye a kasar.