A cikin shirin za a ji cewa, adadin mutanen da suka mutu sakamakon hadarin jirgin ruwa a kogin Victoriya na kasar Tanzaniya, ya kai na mutane 207 ya zuwa wannan rana ta Asabar, inda masu ayyukan ceto suka ci gaba da neman masu sauran rai ko kuma gawawaki.