A cikin shirin za a ji cewar kwancen sojin da Amirka ke jagoranta wajen yaki da kungiyar IS a Iraki da Siriya sun kai jerin hare-hare inda suka lalata wani gida mayakan kungiyar ke hada bama-bamai. Shirin har wa yau ya kunshi shirye-shirye da suka hada da shirin ra’ayin malamai wanda ya maida hankalinsa kan cika kwana 100 da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ta yi.