A cikin shirin za a ji cewa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya kira hukumomin kasar Myanmar da su yi watsi da duk wani mataki da suke dauka kan tsirarun Musulmi 'yan kabilar Rohingya, inda ya ce hukumomin sun dauki mataki ne na kawo karshen tsirarun kasar.