A cikin shirin bayan labaran duniya akwai rahoto kan sabon yunkurin majalisar dokokin Amirka na tsige shugaba Donald Trump daga kujerar mulki da rahoto kan martanin da ake yi a kasar Yemen bayan Amirka ta sanya kungiyar Houthi cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda na duniya da rahoto kan rudanin da ke tattare da sake bude jami’o’in Najeriya saboda sabon rikicin da ya dabaibaye jami’o’in gwamnati.