A cikin shirin za a ji cewa masana tsaro dama al'ummar jihar Zamfara na cigaba da tsokaci kan matakin gwamnatin jihar na ba al'umma dama su mallaki makamai dan su kare kansu daga hare-haren 'yan bindiga. A jihar Agadaez ta Jamhuriyar Nijar an gudanar da taron hukumar kaurar jama'a ta Majalisar Dinkin Duniya domin duba aiyukan ci gaban al'umma da ake yi.