A cikin shirin za a ji cewa mako guda da kaddamar da sabin kudi da aka sakewa fasali a Najeriya har yanzu sabbin kudaden ba su shiga hannun jama’a da dama ba. A Nijar kotun tsarin mulkin kasar ta yi fatali da dokar karin kudin alawus da 'yan majalisar kasar suka yi wa kansu.