Daruruwan mazauna Juba, babban birnin Sudan ta Kudu sun gudanar da zanga zanga a yau, domin nuna adawa da takunkumin hana sayar wa kasar makamai da Amirka ta yi a makon da ya gabata,dai dai lokacin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya umurci jami'an tsaro a Najeriya da su hukunta duk wanda suka tarar yana mallake da makamai ba bisa ka'ida ba.