1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen zaben shugaban kasa a Senegal

January 24, 2012

Abdullahi wade na Senegal ya gabatar da takaransa ne neman shugabancin kasar a wa'adinsa na uku, lamarin da ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar

https://p.dw.com/p/13pHx
Senegal President Abdoulaye Wade, waves at his supporters during a rally in Dakar, Senegal, Friday, Feb. 23, 2007. Wade, who spent three decades in the country's opposition and ran four times for president before winning in a landslide in 2000, says that he's spent a lot of time thinking about what Senegal needs and those that criticize him are failing to see the larger picture. (AP Photo/Schalk van Zuydam)
Shugaba Abdoulaye Wade na SenegalHoto: AP

Shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade ya bayyana aniyarsa na tsayawa takara a zaben kasar wanda za'a gudanar a watan Fabrairu mai zuwa, domin neman wa'adinsa na uku. Wannan mataki dai na tattare sarkakiya sakamakon wata kwaskwarima da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar bayan da shugaban ya hau kujerar mulki a karon farko a shekarar 2000, inda tanadin ya kayyade wa'adin kowane shugaban kasa zuwa biyu kacal. To sai dai shugaban gangamin yakin neman zaben na Wade ya ce ya bada gaskiya cewa kotun tsarin mulkin kasar zata amince da hujjar da suka bayar, wacce ke cewa, ba za'a saka wa'adin mulkinsa na farko a cikin lissafi ba. Tuni dai masu adawa da kungiyoyin farar hula suka yi watsi da wannan hujja suka bukaci da a kiyaye tanadin kundin tsarin mulki. Manyan 'yan takarar da ke neman kujerar shugabancin kasar sun hada da tsoffin shugabani irinsu Moustapha Niasse, Idrissa Seck Macky Sall da mawakin nan mai suna Youssou Ndour da kuma dan adawan nan na Socialisrt Ousmane Tanor Dieng

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba

Edita: Usman Shehu Usman