Shugaba Assad na Syria ya nuna adawarsa da kai hari kan dakarun IS
September 11, 2014Kasashen Larabawa sun mara baya ga Shugaba Barack Obama a kokarin fadada ayyukan kasar Amirka a kan 'yan jihadi a Iraki da Siriya. Amma mahukuntan birnin Damascus sun yi gargadin cewa duk wani ayyukan soji da aka kaddamar a yankinsu za su dauke shi a matsayin hari a kan kasar.
Kasashe 10 ciki har da uwa ma ba da mama cikin kasashen wato Saudi Arabiya sun amince su bada ta su gudunmawar wajen yakar mayakan na IS bayan ganawa da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry da sauran takwarorinsa daga yankin na kasashen Larabawa.
A daidai lokacin da sabuwar gwamnatin hadakar Iraki da bangaren 'yan adawa a Siriya ke lale marhabun da wannan shiri na Shugaba Obama, Shugaban na Siriya Bashar al-Assad da manyan kawayensa Rasha sun yi Allah wadai da wannan yunkuri.
A cewar ministan hadin kan kasa a Siriya Ali Haidar "duk wani yunkuri da aka yi ba tare da sanin gwamnatin ta Siriya ba hari ne kawai kan kasar."