Shugaba Bush ya ce Isra'ila da Palasɗinawa ne kaɗai zasu iya samar da zaman lafiya tsakaninsu
January 10, 2008Talla
Shugaban kasar Amurka George Bush ya bukaci Israilawa da Palasɗinawa da su yi anfani da damar da ake da ita yanzu don samarda zaman lafiya tsakaninsu. Wajen wani taron manema labarai da firaminista Ehud Olmert a birnin Ƙudus,Bush ya ce jama’ar Israila da na Palasdinawa ne kaɗai zasu iya ɗaukar ƙwararan matakai na samarda kasashe biyu makwabtan juna. Sai dai hare-hare ta sama da Israila ta ke kaiwa da kuma kuma hare haren roka na martani daga zirin Gaza suna kawo cikas ga shirin zaman lafiyar. Olmert yace ba za a samu zaman lafiya ba muddin dai an ci gaba da kai hare haren rokoki daga zirin gaza.
A yau Bush zai wuce zuwa gaɓar Yamma da kogin Jordan inda zai tattauna da shugaban Palasɗinawa Mahmud Abbas.