Sabbin gwamnoni a Sudan ta Kudu
December 30, 2015Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir ya bukaci sabbin gwamnonin da aka nada a kasar su tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi tsakanin gwamnatinsa da bangaren 'yan adawa a karshen watan Agusta.
Da yake jawabi a lokacin rantsar da sabbin gwamnonin a ranar Talata shugab Kiir ya bayyana cewa ba zai lamunci duk wani yunkuri na cin hanci da rashawa ba, abin da ya bayyana da zama cutar daji a kasar .
"Muna bukatar gwamnati mai inganci, haka kuwa abu ne da zai samu ta hanyar shugabanci nagari, wanda babu batun cin hanci da rashawa a cikinsa, abinda ke zame mana tamkar cutar daji wacce zamu tashi tsaye baki daya mu yi yaki da ita".
A ranar 24 ga watannan na Disamba ne dai shugaba Kiir ya rushe jihohi 10 na Sudan ta Kudu da samar da sabbin jihohi 28 a yunkurin da ke shan suka ta 'yan adawa.