Shugaba Macron na Faransa ya fara ziyara a China
January 8, 2018Shugaba Emmanuel Macron na Faransa a wannan rana ta Litinin ya kaddamar da fara ziyarar aiki a birnin Xian na China inda ya fara ziyarar wannan birni mai tarihi gabannin gabatar da jawabinsa da zai tabo dangantaka tsakanin China da Faransa.
Shugaba Macron da ya fara ziyarar ta kwanaki uku a wannan birni bisa jagorancin mai masaukin bakinsa Shugaba Xi Jinping na China inda za su mayar da hankali kan batutuwa da suka shafi tsare-tsare na kasuwanci tsakanin kasashen na yankin Asiya da takwarorinsu na kasashen Turai ta hanyar musayar kayayyaki na kasuwanci da bin hanyoyin ruwa da jiragen kasa da na mota.
Tsarin kasuwancin da a China aka fi sani da "One Belt One Road" ana masa fata ganin ya hada kasashen Tsakiyar Asiya da wajenta. Shugaba Macron dai bayan ziyarar birnin na Xian zai kuma ziyarci birnin Beijing tare da tawagar mutane 60 ta 'yan kasuwa da cibiyoyi.