Shugaban Tanzaniya ya rage albashin jami'an gwamnatinsa.
October 4, 2017Shugaban John Magufuli ya sanar da rage albashin manyan mukaraban gwamnatinsa inda ya kuma bukaci wadanda suka ki amincewa da matakin da su gaggauta ajiye mukaminsu, Magufuli ya kuma yi watsi da bukatar wasu daga ciki na neman karin alawus bisa wasu dalilai na rashin abubuwan more rayuwa da ya ce al'ummar kasar ke fuskanta, ya kuma kare matakin rage albashin ganin yadda wasu bayanai ke nuni da cewa akwai wasu 'yan tsiraru da ke wawashe kudadden gwamnati.
Shugaban ya kuma baiyana cewa albashinsa a wata guda dala dubu hudu ne kacal bayan ya rage albashin da ya kamata ya karba, hakan na nufin shi ne shugaban Afirka mafi kankantan albashi a nahiyar. Tun bayan dare karagar mulki a shekarar 2015, Magufuli y ke yaki da masu yin almundahana da kudadden gwamnati a kasar ta Tanzaniya.