ANC: Sake bai wa Ramaphosa shugabanci
December 16, 2022Talla
Rahotanni sun nunar da cewa wakilan mambobin jam'iyyar ta ANC mai mulki a Afirka ta Kudun dubu hudu da 500 daga sassan kasar dabam-dabam, na shirin kada kuri'a a yayin taron na kwanaki biyar da ke gudana a wani wajen taro kusa da birnin Johannesburg. Shugaba Cyril Ramaphosa na neman yin tazarce a shugabancin jam'iyyar ta ANC, a daidai lokacin da take fuskantar kalubale sakamakon raguwar magoya baya da ta ke fuskanta bayan tsahon shekaru 28 tana mulki a kasar.