Shugaba Rousseff na dakon makomarta a Brazil
August 30, 2016A ranar Talatan nan Shugaba Dilma Rousseff za ta ji hukuncinta a majalisar dattawan kasar Brazil bayan zaben da 'yan majalisar za su kada da ake saran zai yi gaba da kujerar shugabar duk kuwa da ikirarin da take yi na cewa an mata juyin mulki ne .
Shugabar da ke zama mace ta farko da ta jagoranci kasar ta Brazil bayan musayar kalamai da 'yan majalisar a ranar Litinin ta ce ba ta da laifi kan zarge-zargen rashin iya tafiyar da mulki da ake mata, kuma idan har ta kai kasa to dimokradiya a kasar na fiskantar babbar barazana.
'Yan majalisar dai a ranar Talatan nan za su ji daga lauyoyi daga dukkan bangarori biyu, kafin su shiga muhawara da za ta kai ga kada kuri'ar da ake tsammanin ganin biyu bisa uku ko 54 daga cikin 'yan majalisa 81 sun zabi cire shugabar daga mulkin Brazil.