1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Salva Kiir ya nada sabon mataimaki

Gazali Abdou TasawaJuly 26, 2016

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya sanar da nada Taban Deng a matsayin sabon mataimakinsa domin maye gurbin babban abokin hamayyarsa Riek Machar wanda ya fice daga babban birnin kasar na Juba

https://p.dw.com/p/1JVpA
Südsudan Salva Kiir Mayardit
Hoto: Getty Images/AFP/M. Sharma

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya sanar da nada a jiya Litinin Taban Deng a matsayin sabon mataimakinsa domin maye gurbin babban abokin hamayyarsa Riek Machar wanda ya fice daga babban birnin kasar Juba bayan kazamin fadan da ya hada sojojin mutanen biyu a farkon wannan wata na Yuli.A ranar Asabar da ta gabata ne dai wani bangare na shugabannin tsohuwar kungiyar 'yan tawayen ta ba da sunan Taban Deng wanda ke rike da mukamin ministan ma'aikatar ma'addinai a gwamnatin hadin kan kasa domin maye gurbin Riek Machar idan har ya yi ya dawo a birnin na Juba.Wannan nadi na Taban Deng na kara nuni da tabbatar da barakar da ta samu a cikin tsohuwar kungiyar tawayen kasar ta Sudan ta Kudu. Tuni dai Riek Machar ya yi watsi da wannan nadi na Taban Deng.