Shugaba Trump na ziyara a Koriya ta Kudu
November 7, 2017Talla
Gananawar Trump da Moon Jae-In na da nufin shawo kan sabanin da ke da akwai tsakaninsu musamman kan batun Koriya ta Arewa.
A watan Satumban da ya gabata ne dai, Shugaba Trump ya zargi takwaransa na Koriya ta Kudu Moon Jae- In wanda ke da ra'ayin sasantawa da Koriya ta Arewa da kasancewa mai gurguwar siyasar neman zaman lafiya maras amfani.
Sai dai a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter daga kasar Japan inda ya kai ziyarar farko kafin zarcewa zuwa Koriya ta Kudun Trump ya sha alwashin samun fahimtar juna da takwaran nasa wanda a wannan karo ya bayyana shi da kasancewa mutuman daraja.
Batun nukiliyar koriya ta Arewa zai kasance a sahun gaban muhimman batutuwan da za su tattauna a kai.