Shugaba Trump ya yaba wa NATO
July 6, 2017Talla
Shugaban na Amirka ya yi kira ga kasar Rasha da ta guji munanan ayyukan da ta ke yi a Ukraine da ma wasu kasashen duniya.
A jawabin da ya gabatar a birnin Warsaw, Mr. Trump ya yi kiran hadin kan kasashen yamma don tunkarar barazanar tsaro da kasashen ke fuskanta.
Ya yi gargadi da kakkausar lafazi kan barazanar tsaro da manyan kasashen ke ciki, yana mai saba misalai da wasu hare-haren da ke wakana a wasu kasashen nahiyar Turai.
Cikin kalaman Mr. Trump, ya ce akwai matukar barazana ga rayuwar al'umar manyan kasashen, sai dai ya ce za su yi nasara kan masu hare-hare.