1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dos Santos zai yaji mulkin Angola

February 3, 2017

Shugaba Jose Eduardo dos Santos na kasar Angola zai ajiye madafun iko bayan mulki na kusan shekaru 40 a kasar da ke kudancin Afirka.

https://p.dw.com/p/2WvcS
Angola Jose Eduardo dos Santos
Hoto: picture alliance/AP Photo/T. Hadebe

Shugaba Jose Eduardo dos Santos na kasar Angola ya tabbatar da cewar ba zai sake neman shugabancin kasar ba, yayin zaben watan Agusta da ke tafe. Shugaban wanda ya shafe shekaru 37 kan madafun iko, ya nunar da cewa ministan tsaron kasar zai gaji mukamin. Jose Eduardo dos Santos dan shekaru 74 ya kasance daya daga cikin mutanen da suka fi dadewa kan madafun iko a nahiyar Afirka baki daya.

Dos Santos ya shaida wa taron jam'iyyar MPLA mai mulki da ya gudana a birnin Luanda cewar an amince da sunan Joao Manuel Goncalves Lourenco ministan tsrao a matsayin wanda zai jagoranci jam'iyyar domin neman shugabancin kasar. Tun farkon wannan shekara shugaban ya tabbatar da cewar zai ajiye madafun ikon kasar cikin shekara mai zuwa ta 2018.

A shekara ta 2002 gwamnatin kasar ta Angola ta samu nasarar kawo karshen yakin basasa.Tun bayan samun 'yanci daga Turawan mulkin mallaka na Portugal mutane biyu suka mulki kasra ta Angola, wato sshugaba na farko  Agostinho Neto wanda ya rasu kan madafun iko, kuma tun bayan mutuwar Jose Eduardo dos Santos ke rike da ragamar mulkin kasar.