Shugaban Brazil ya yanki jiki ya fadi
December 24, 2019Talla
An garzaya da Shugaba Jair Bolsonaro na kasar Brazil zuwa asibiti bayan da ya fadi saboda da rashin lafiya a fadar shugaban kasar. A daren wannan Litinin da ta gabata aka garzaya da Bolsonaro zuwa wani asibitin soja da ke birnin Brazilia babban birnin kasar inda aka gudanar da bincike kan shugaban, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta nuna.
Shugaban zai ci gaba da zama a asibiti har zuwa tsawon rabin rana. Kafofin yada labaran Brazil sun ruwaito cewa Shugaba Jair Bolsonaro ya fadi ne lokacin da yake wanka inda ya buga kansa, tun farkon wannan watan shugaban yake bayyana wa mashawartansa yana jin gajiya.