Shugaban Falasdinawa ya bukaci gani a kasa
December 27, 2016Bukatar hakan dai na zuwa ne bayan da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci Isra'ila ta tsaida duk wasu gine-gine da ta ke yi a yankin.
Wannan matsaya dai da kwamitin sulhun ya cimma na zama ginshiki na abin da za a dora tattaunawa mai muhimmanci kan rikicin na Falasdinawa da 'yan Isra'ila, tattaunawar zaman lafiyar da za ta zama ta kasa da kasa da Faransa za ta jagoranta.
Abbas ya ce ya na fatan tattaunawar da za a yi ranar 15 ga watan Janairu za ta zama sila ta kawo karshen mamaya da Isra'ila ke yi a yankin na Yammacin Kogin Jodan da Gabashin Jerusalem. A ranar Juma'a ce dai Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya bayan zama mambobi 14 na kwamitin suka amince da bukatar, yayin da Amirka ta zama 'yar ba ruwanta, abin da ya sanya Isra'ila ta maida martani mai zafi.