1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Faransa na ziyara a Iraki

September 12, 2014

Shugaban Faransa ya fara wata ziyara a Iraki gabannin shirin Amirka da kawayenta na afkawa kungiyar nan ta IS da ke rajin kafa daular Musulunci a Iraki da Siriya.

https://p.dw.com/p/1DB8z
EU Gipfel - Francois Hollande
Hoto: Getty Images

Masu aiko da rahotanni sun ce Shugaba Francois Hollande ya sauka a birnin Bagadaza da sanyin safiyar Juma'ar nan tare da ministocinsa na tsaro da na harkokin kasahsen ketare inda ake ya gana da firaministan da kuma shugaban kasar ta Iraki.

Tattauna bangarorin biyu dai na da nasaba da kokarin Faransa na bada tallafinta wajen yakar 'yan kungiyar ta IS, kuma da zarar Irakin ta amince ake sa ran dakarun Faransa za su afkawa wuraren da IS din ke rike da su.

Wannan dai na zuwa ne gabannin wani taro da za a gudanar a birnin Paris na Faransa kan kasar ta Iraki wanda ake kallo a matsayin wani yunkuri na gwamnatin Faransa na karfafa gwamnatin Irakin da kuma karya kashin bayan kungiyoyin masu kaifin kishin addini.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman