Shugaban gwamnatin Jamus zai sake tsayawa takara
November 22, 2024Talla
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya shirya yi wa jam'iyyarsa ta SPD takara a zaben kasa da za a shekarar da ke tafe.
Jam'iyyar tasa ta Social Democrats, ta ce a ranar Litinin na makon gobe ne za a tsayar da Olaf Scholz domin fafatawa a zaben.
Hakan dai ya biyo rashin amincewa da takarar da ministan tsaron Jamus Boris Pistorius ya yi.
Shi dai Pistorius wanda shi ne babban mai neman takarar da shugaban gwamnatin, ya ce Olaf Scholz ne zai fi dacewa da neman matsayin.
Cikin watan Fabrairun badi ne dai za a yi zaben na Jamus, bayan rugujewar gwamnatin kawancen jam'iyyu uku a cikin wannan wata na Nuwamba.