1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban gwamnatin Nijar ya gana da matasan Diffa domin kashe wutar rikicin da ya barke

April 28, 2013

Matasan jihar Diffa mai arzikin man fetur a Nijar, sun shiga gwagwarmayar kwatar 'yancin da su ka ce an tauye masu wajen daukar ma'aikata a kamfanin hakar mai.

https://p.dw.com/p/18ObP
Nigerian Prime Minister Niger Brigi Rafini (L) before a bilateral meeting at the EU headquarters in Brussels on June 06, 2012. AFP PHOTO/JOHN THYS (Photo credit should read JOHN THYS/AFP/GettyImages)
Brigi Rafini , Ministerpräsident Niger 2012Hoto: Getty Images

A birnin Diffa dake gabashin Jamhuriya Nijar, an yi mummunar arangama tsakanin matasa masu zanga-zanga da jami'an tsaro.Ta la'akari da yadda wannan rikici ya dauki saban sallo, tuni Firaministan Nijar Briji Raffini ya sauka birnin Diffa ranar Asabar da yamma.

Matasa sun shirya wannan zanga-zanga domin nuna fushi game da bambanin da suka ce gwamnati na nunawa wajen daukar ma'aikata a kamfanonin hakar mai dake jihar ta Diffa,kamar yadda Djidda Ari daya daga jagoran masu zanga-zangar ya shaida wa DW ta wayar talho.

Saidai a yayin da shugaban Biriji Raffini, ke kokarin kashe wutar rikicin zanga-zangar matasan birnin Diffa,rikicin ya bulla a Gegimi dake kusa da iyaka da kasar Chadi.

Rahotani da suka zo mana daga Gegemi sun ce masu zanga-zangar sun kona ma'aikatar shari'a, kamar yadda Atta Haske wani mazaunin garin ya shaidar.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Saleh Umar Saleh