Shugaban Jamus ya jaddada goyon bayan ga gwamnatin Habasha
January 28, 2019Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier, ya samu tarba irin ta girmamawa ta faretin soji a Adis Ababa babban birnin kasar Habasha. Shugabar kasar Habasha Sahle-Work Zewde ce ta marabci tawagar Steinmier bayan ganawarsa da firaminista Abiy Ahmed. To ko me ya banbanta a idanun Shugaba Steinmeier a wannan ziyarar bayan zuwansa kasar shekaru 6 baya a matsayin ministan harkokin wajen Jamus?
Ziyarara Steinmeier a Habasha, ta kunshi ganawar jinjina ga firamista Abiy Ahmed, kan yunkurin farfado da martabar kasar ta kawo karshen fahimtar juna tsakanin kabilu, da ma warware takaddamar siyasar gaba a kasar. Ziyarar ta Steinmier ta ta samu rakiyar 'yan kasuwa daga kamfanin kera motocin VV da kamfanin Siemens, domin ganawa da 'yan kasuwar Habasha kan dangantakar kasuwancin tsakanin kasashen biyu. Sai dai manema labarai sun yi amfani da wannan dama ta jin inda aka kwana kan batun girka kamfanin VV da sauran kamfanonin Jamus a Habsha. Amma Shugaba Steinmeier ya bayyana matsalolin da ke hana ruwa gudu a dangantakar kasuwancin kasa da kasa.
Abiy Ahmed mai shekaru 42, ya kaddamar da jerin sauye sauye a kasar Habasha, cikin har da yaki da cin hanci da 'yancin fadin albarkacin baki hada da bude kofofi ga harkar kasuwaci da sauran aksasehn duniya domin tada komadar tattalin arzikin da ya shiga wani yanayi na rashin tabbas. firamistan ya kuma samu lambar yabo kan cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta abokiyar hamayyar Habasha wato Iritriya tare da sako dubban fursunonin siyasa da ba da damar shiga tattaunawa da 'Yan adawa.