Shugaban kasar Amirka ya bayyana shakku game da Isra'ila
February 11, 2018Talla
Donald Trump ya kuma kara da cewar duk da cewar akwai kyakyawar dangantaka tsakanin Amirka da Isra'ila,sulhuntawa da Falasdinawa za ta kara dankon alakar kasashen biyu. A baya dai shugaba Trump ya yi Allah wadai da Falasdinawa lokacin da su ka shaidawa duniya cewar ba bu sauran batun sulhu tsakanin su da Isra'ila bayan bayana birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar ta Isra'ila.