Omar al-Bashir na ziyara a Katar
January 22, 2019Talla
Kamfanin dillancin labarai a kasar ta Katar ya bayyana cewa Shugaba Omar al-Bashir zai isa kasar ta Katar a ranar Talata kana ya gana da masaraucin da ke mulkin kasar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani a ranar Laraba.
A wata hira da shugabannin suka yi ta wayar tarho a ranar 22 ga watan Disamba, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta tallafa wa Sudan saboda halin da ta fada don ta samu waraka kamar yadda kamfanin dillancin labaran Sudan ya ba da rahoto.Tun dai a 1989 da al-Bashir ya yi juyin mulki a Sudan ya ci gaba da mulki a kasar har kawo wannan lokaci.