1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Kenya ya kalubalanci fannin shari'a

Yusuf Bala Nayaya
September 2, 2017

Shugaban na Kenya ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce abin da ya rage yanzu shi ne su sake haduwa da bangaren adawa a akwatin kada kuri'a.

https://p.dw.com/p/2jFpn
Kenia Wahl Annullierung Uhuru Kenyatta
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Kenya TV

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana cewa zai sake fita neman kuri'ar 'yan kasar sai dai ya ce akwai matsala a tsarin shari'a na kasar kuma dole ne a gyara, kalaman da ke zuwa bayan da kotun kolin kasar ta rushe sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a watan da ya gabata, kana ta ba da umarni a sake gudanar da zabe cikin kwanaki 60.

Shugaba Kenyatta dai kafin furta wadannan kalamai ya gana da gwamnoni da wasu zababbun jami'ai na jam'iyyarsa. Sai dai ya ci gaba da jaddada kalamansa na ranar Juma'a cewa zai ci gaba da mutunta hukuncin da kotu ta yanke da ke zama fitacce a Afirka, inda hukuncin kotuna ke zama sai abin da ya yi dadi ga bangaren masu mulki.