1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Kenya ya samu sabon wa'adi

August 12, 2017

Hukumar zaben Kenya ta tabbatar da cewa shugaba Uhuru Kenyatta ya sake lashe zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/2i6bu
Kenia Unruhen nach dem Wahlenergebnis
Hoto: Getty Images/AFP/P. Meinhardt

An samu zanga-zanga da tashe-tashe hankula a wasu sassan kasar Kenya, yayin da a wasu sassan mutane suka sheke da murna, bayan hukumar zaben kasar ta Kenya ta tabbatar da Shugaba Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar a karo na biyu.

Shugaban hukumar zaben kasar Wafula Chebukati ya bayar da sanarwar inda shugaba Kenyatta ya samu nasara da lashe kashi 54 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da jagoran 'yan adawa Raila Odinga ya samu kashi 44 cikin 100 na kuri'un. An dai jibge daruruwan 'yan sanda a birnin Nairobi fadar gwamnatin kasar, domin tabbatar da doka da oda, yayin da magoyan bayan jagoran 'yan adawa Raila Odinga ke nuna rashin yarda da sakamakon. Shi kansa shugaba Uhuru Kenyatta dan shekaru 55 ya yi kan hakin kan kasa tare da neman 'yan adawa su yi aiki tare.