Kungiyar Taliban ta tabbatar da mutuwar Jalaluddin Haqqani
September 4, 2018Talla
Karkashin jagorancin shugaban na Haqqani, mayakan kungiyar sun kai munannan hare-hare na kunar bakin wake da suka janyo asarar daruruwan rayuka, hakazalika kungiyar ta yi kaurin suna a kisan manyan jami'an gwamnatin Kabul da kuma yin garkuwa da turawa don neman kudin fansa.
Wannan dai ba shi bane karon farko da ake fidda sanarwar mutuwar jagoran kungiyar. Yanzu dai rahotannin na cewa dan jagoran mai suna Sirajudin Haqqani ya maye gurbin mahaifinsa. Jalaludin Haqqani abokin kawance ne na kungiyar al-Qaida da kuma kungiyar Taliban.