Tazarce a Rasha
March 10, 2020Talla
Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya nuna bukatar gyara ga kundin tsarin mulki domin ya samu ta zarce har zuwa shekara ta 2036, amma ya ce yana son ganin an takaita wa'adin shugaban kasa idan tsarin dimukaradiyyar kasar ya karfafa. Haka na zuwa yayin da majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar amincewa da gyara ga kundin tsarin mulkin. Wannan shi ne mataki na biyu daga cikin matakai uku da ake bukata kafin mika wa majalisar dattawa.
Shugaba Vladimir Putin na Rasha dan shekaru 67 da haihuwa yana kan madafun iko kimanin shekaru 20 da suka gabata tun daga inda daga ciki ya rike mukamun firaminista na wani lokaci.