Shugaban sojoji ya gargadi jam'iyyar Mugabe
November 13, 2017Talla
Shugaban rundinar sojan kasar Zimbabuwe a wannan rana ta Litinin ya bukaci a dakatar da kore-kore da ake a jam'iyyar ZANU-PF, abin da ke zuwa bayan korar mataimakin shugaban kasa Emmerson Mnangangwa, ya kuma yi gargadin cewa soja na iya kawo dauki a rudanin da kasar ke neman fadawa.
Kore-koren da ake yi wanda ke da buri na kakkabe wasu kusosi a jam'iyyar ta masu mulki ya zama dole a tsayar da shi take a cewar Janar Constantino Chiwenga a lokacin da yake jawabi a taron manema labarai wanda kimanin manyan sojoji a kasar 90 suka halarta a hedikwatar sojan kasar ta Zimbabuwe.
A cewarsa wadanda ke neman haifar da rudani a kasar su kuka da kansu, idan har suka nemi dagula lamura ya zama dole soja su sa hannu don gudun kada a wargaza kasar.