Shugaban sojojin Zimbabuwe ya yi murabus
December 18, 2017Talla
Shi dai tsohon shugaban sojojin shi ne ya jagoranci kawar da gwamnatin Robert Mugabe wanda ya shafe shekaru 37 ya na mulkin kasar ta Zimbabuwe. Jagoran sojin ya bayyana hakan ne yayin da ya ke wani jan kunne ga 'yan jam'iyyar ZANU-PF inda ya ke cewar sojojin kasar a shirye suke kowanne lokaci don murkushe kowanne irin rikici a jam'iyyar.