Shugaban Sudan ta Kudu ya bayyana fata kan tsagaita wuta
September 15, 2015Shugaba Salva Kiir na kasar Sudan ta Kudu ya bayyana cikakken goyon baya kan shirin samar da zaman lafiya, yayin da kasar Amirka ke shirin neman Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya saka wa kasar takunkumi. Lokacin da yake magana da manema labarai a birnin Juba fadar gwamnatin kasar shugaban ya dage kan cewa ya ba wa sojojin kasar umurnin tsagaita wuta.
Wannan yana zuwa lokacin da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya gayyaci bangarorin na Sudan ta Kudu zuwa taron majalisar. Ban ya gayyaci Shugaba Salva Kiir da jagoran 'yan tawaye Riek Machar zuwa taro na musamman kan tsagaita wuta a Sudan ta Kudu da zai gudana cikin wannan wata na Satumba.
A karshen shekara ta 2013 Sudan ta Kudu ta fada cikin yakin basasa lokacin da Shugaba Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa da yunkurin kifar da gwamnati, abin da ya zama rikici tsakanin manyan kabilun kasar.