Shugaban Sudan zai ziyarci Sudan ta Kudu
April 12, 2013Ziyarar wace ita ce ta farko da shugaban na Sudan zai kai a yar ƙaramar ƙasar da ta sami yanci gashin kai, bayan wata ƙuria ta raba gardama da aka yi a cikin watan Yuli na shekara ta 20011.Na zaman wata kafa ta ƙara ƙarfafa hulɗa da dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, bayan da aka kwashe lokaci mai tsawo suna kabsa yaƙin basasa kafin ɓalewar Sudan ɗin ta Kudu.
An shirya shugabannin biyu zasu tattauna batun tsaro da na yanki Abyei mai arzikin man fetir wanda ƙasashen biyu ke iƙirarin mallaka. A makon jiya ne dai hukumomin Sudan ta Kudu suka sanar da sake tura man fetir ɗin da suke haƙowa zuwa Sudan. Tun da farko an dakatar da shirin ne kusan shekara guda akan zargin da Sudan ta Kudu ɗin ta yi cewar Sudan na tswala kuɗaɗen fito tare kuma da satar man na su.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman