1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Taliban ya gargadi kasashen waje

Mouhamadou Awal BalarabeJuly 2, 2016

Shugaban Taliban Haibatullah Akhundzada ya yi kira ga kasashen waje da su kawo karshen mamayar da suke yi wa Afghanistan idan suna so a zauna lafiya a kasar.

https://p.dw.com/p/1JHxc
Afghanistan Mullah Haibatullah Achundsada
Hoto: picture-alliance/dpa/Afghan Islamic Press via AP

Sabon shugaban Taliban Haibatullah Akhundzada ya bukaci gwamnatin Amirka da ta kawo karshen mamayar da take yi wa kasar Afghanistan, idan tana so su sulhunta rikicin da ke tsakaninsu cikin ruwan sanyi. Cikin wani jawabi da ke zama na farko tun bayan nadashi, Mollah Akhundzada ya jadadda bukatar gudanar da mulki bisa tafarkin shari'ar Musulunci a Afghanistan, ba a kan tafarkin manufofin kasashen yammacin duniya ba.

Sannan kuma ya yi amfani da wannan dama wajen nuna yiwuwar fahimtar juna tsakaninsa da hukumomin Kabul, idan gwamnatin ta Afghanistan ta raba gari da manyan kasashen duniya. Shugaban na Taliban ya ce burinsa shi ne kafa hadaddiya kuma 'yantaciyar kasar Afghanistan mai bin shari'a sau da kafa.

Su dai 'yan Taliban sun samu nasarori da dama a shekarar da ta gabata a fagen yaki, bayan da dakarun Amirka suka fara janyewa daga Afghanistan. Sai dai yanzu haka akwai sojojin kawance dubu 13 da ke jibge a kasar ciki kuwa har da dakarun Amirka dubu 13.