An bayyana sakamakon zaben tsibirin Zanzibar na Tanzaniya
March 21, 2016Talla
Hukumar zaben tsibirin Zanzibar mai kwarya-kwaryar 'yanci daga Tanzaniya, ta bayyana Shugaba Ali Mohamed Shein wanda yake kan madafun iko a matsayin wanda ya sake lashe zaben karshen mako.Shein na jam'iyyar Chama Cha Mapinduzi mai mulki ya samu kashi 91 cikin 100 na kuri'un da aka kada, kuma tun farko 'yan adawa sun janye daga zaben. 'Yan adawa sun yi zargi tabka magudi a zagayen farko na zaben abin da ya janyo suka kaurace wa zagaye na biyu.
Shi dai Ali Mohamed Shein ya samu sabon wa'adi na mulki, inda aka fara zabensa a shekara ta 2010.