1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar tashi tsaye domin kare muhalli

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 23, 2019

Dalibar nan 'yar asalin kasar Sweden Greta Thunberg da ta fara kaddamar da gangamin yaki da sauyin yanayi mai taken "Fridays for Future," ta zargi shugabannin kasashen duniya da kwayewa manyan gobe baya.

https://p.dw.com/p/3Q7UB
UN-Klimagipfel New York | Angela Merkel & Greta Thunberg
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da matashiya mai fafutukar kare muhalli Greta Thunberg Hoto: Reuters/Steffen Seibert/Bundesregierung

Thunberg ta bayyana hakan ne yayin taron da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guterres ya kira, kan sauyin yanayi a birnin Newe York na Amirka, inda ta ce shugabannin sun kwaye musu baya ta hanyar gaza magance matsalar fitar hayakin masana'antu da ke gurbata muhalli. Greta Thunberg dai ta gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. Guterres ya kira wannan taron ne da nufin zaburar da shugabannin kasashe kan bukatar tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar kare muhallin da aka cimma a birnin Paris na kasar Faransa, yarjejeniyar da kasashe 66 suka amince da ita ta hanyar shan alwashin dakile gurbatar muhallin nan da shekara ta 2050. Sai dai shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro da a yanzu haka ksarsa ke fuskantar babbakewar dajin Amazon da ke da matukar muhimmanci ga iskar da duniya ke samu, bai halarci wannan taron ba. A jawabinsa shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis ya bukaci shugabannin al'umma da su tabbatar sun dauki matakan yaki da sauyin yanayin da gaskiya, kasancewar sauyin yanayin na zaman babbar barazana da duniya ke fuskanta.