1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin Afirka sun ja hankalin sojin Sudan

Abdullahi Tanko Bala
April 23, 2019

Taron kolin shugabannin na Afirka ya bukaci sojoji da ke jan ragamar mulkin Sudan su hanzarta aiwatar da shirin mayar da kasar kan turbar dimukuradiyya cikin watanni uku.

https://p.dw.com/p/3HIlo
Ägypten Kairo - Gipfeltreffen
Hoto: Reuters/The Egyptian Presidency

Shugabannin sun baiyana wannan bukata ce ne a karshen taron kolin da suka gudanar a wannan talatar a birnin Alkahira. Kasar Masar da sauran wakilan kasashen Afirka sun amince da bukatar karin lokaci ga hukumomin Sudan da 'yan siyasa su aiwatar da shirin mayar da kasar ga mulkin farar hula cikin kwanciyar hankali da lumana.

A sanarwar bayan taro da suka fitar shugabannin sun kuma yi kira ga kungiyar tarayyar Afirka ta kara wa majalisar mulkin sojin watanni uku kan wa'adin da ta bayar tun da farko wanda zai cika a karshen wannan watan na Afrilu domin baiwa sojojin damar mika mulkin ga farar hula cikin tsanaki ko kuma a dakatar da kasar daga wakilci a cikin kungiyar ta tarayyar Afirka. Wannan a cewar sanarwar zai sassauta matsin lambar da kasashen duniya ke yiwa majalisar sojin ta mika mulki ga farar hula.

A ranar 11 ga wanann watan na Afrilu ne sojoji suka hambarar da shugaba Omar al Bashir daga karagar mulki, sai dai duk da haka masu zanga zanga sun cigaba da yin gangami suna bukatar sojoji su gaggauta mayar da mulki ga farar hula, bukatar kuma da majalisar sojin ta yi turjiya akai. Shugabannin kasashe da manyan jami'ai daga kasashen Habasha da Najeriya da Rwanda da kuma Afirka ta Kudu suka halarci taron.