Shugabannin Isra'ila na nazarin sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta
July 17, 2014Wani jami'in Isra'ila ya ce manyan wakilan kasar da ke tattaunawa a birnin Alkahira sun amince da shawarar da Masar ta bayar na tsaigaita wuta gaba daya a rikicin Gaza daga asubahin ranar Jumma'a: To sai dai jami'in ya ce dole sai shugabannin Isra'ila sun yarda da shirin. Jami'in wanda da farko ya ce majalisar tsaron Isra'ila ta amince da shirin, daga bisani ya fada wa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa majalisar ba ta kada kuri'a ba kuma tana kan nazarin ka'aidojin yarjejeniyar. Har wannan lokaci dai ba bu wani labari daga Hamas ko wasu kungiyoyin Falasdinawa daga Gaza na ko sun amince da shirin tsagaita wuta na dindindin don kawo karshen barin wutar da a wannan Alhamis ya shiga kwana na 10. Sai dai an jiyo Hamas na musanta labarin da rundunar sojin Isra'ila ta bayar cewa wasu rokoki uku da aka harba daga Gaza sun fadi a kudancin Isra'ila sa'o'i biyu bayan fara shirin tsagaita wuta na jin kai.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Suleiman Babayo