Shugabar Brazil za ta gana da masu zanga-zanga
June 22, 2013Shugabar ta bayyana haka ne a wani jawabin da ta yi a daran jiya ta gidan talabijin da rediyo na ƙasar, tare da yin Allah wadai da yamutsin da ke faruwa:
Ta ce : ''Ya 'yan ƙasata Brazil ba za mu iya ci gaba da kasance wa cikin wannan hali na tashin hankali ba, wanda ka iya mayar da ƙarsarmu baya. Ta ce zamu yi amfani da ƙarfin doka ta kowane hali, domin yaƙi da kwasar ganima da fashi da jama'a ke yi a kan dukiyar gwamnati, domin yin hakan ya saɓama demokraɗiyya.''
Masu yin boren na kokawa ne da matsalar cin-hanci da ta zama ruwan dare da tsadar rayuwa da kuma maƙuden kuɗaɗen da ake kashewa, domin gina filayen wasan kwallon kafa. To amma shugabar ta kare shirin, kuma hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ce ba za a fasa yin gasar kwallon kafa ta nahiyoyin da ake yi a ƙasar ba, da kuma ta duniya da za a yi a nan gaba.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman