1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabar kasar Brazil na cikin tsaka mai wuya

April 12, 2016

Wani kwamiti na 'yan majalisar dokokin kasar Brazil mai membobi 65 ya kada kuri'ar amincewa da ci gaba da tattauna kudirin tsige shugaba Dilma Rousseff daga mukaminta.

https://p.dw.com/p/1ITao
Brasilien Präsidentin Dilma Rousseff
Shugabar kasar Brazil Dilma RousseffHoto: picture-alliance/dpa/F. Bizerra Jr.

Kwamitin na musamman mai membobi guda 65 ya amince da mafi yawan kuri'u kan wannan mataki wanda zai bai wa 'yan majalisun dokokin damar tattaunawa tare da kada kuri'ar tsige shugabar kasar ko kuma akasin hakan a ranar Lahadi mai zuwa.

Bayan da suka shafe awowi 11 suna mahawarori masu zafi, har da zage-zage, an samu 'yan majalisu 38 da suka aminta da daukan matakin tsige shugabar yayin da 27 suka kada kuri'un kin amincewa da wannan tsari. Sai dai yayin wani taron gangami na bangaran masu goyon bayan shugabar kasar, sun kira wannan mataki a matsayin juyin mulki kuma a cewarsu amincewar kwamitin ba wai yana nufin za su samu nasarar yin abin da suke so ba.