Bashar al-Assad ya isa kasar Saudiyya
May 18, 2023Wannan dai na alamta komawar Shugaba Bashar al-Assad da kasarsa Siriya cikin kungiyar ta kasashen Larabawa bayan mayar da ita saniyar ware, sakamakon yakin basasar da ta sha fama da shi a yayin guguwar juyin-juya halin da ta tashi a kasashen Larabawan. Rahotanni sun nunar da cewa Assad ya isa birnin Jeddah na Saudiyya, kwana guda gabanin taron kungiyar mai mambobi 22. Wannan dai na zuwa ne makonni biyu bayan da kungiyar ta amince da komawar Siriyan cikinta, abin da ya kawo karshen dakatarwar da aka yi mata na tsawon shekaru. Saudiyya da ke zaman mai masaukin baki a taron, na daga cikin kasashen da suka goyi bayan 'yan tawayen Siriyan masu dauke da makamai da ke kokarin kifar da gwamnatin Assad din a yayin yakin basasar da Damascus ta tsinci kanta a ciki.