1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya ta ce Amirka na yin fuska biyu

September 29, 2014

Ministan harkokin kasashen ketare na Siriya Walid al-Moallem ya soki lamirin kasar Amirka dangane da jagorancin yakar 'yan kungiyar IS.

https://p.dw.com/p/1DNJO
Hoto: picture alliance/dpa/Matthew Bruch

Al-Moallem ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi ga taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya. Ya ce Amirka na yin fuska biyu ne ta hanyar yakar 'yan ta'adda a hannu guda yayin da take baiwa 'yan tawaye makamai da kudaden gudanar da ayyukansu a daya hannun inda ya ce hakan babu abun da zai haifar sai kara tabarbarewar al'amura da kara ta da zaune tsaye da ma sake samar da wata kungiyar ta masu tsattsauran ra'ayi. Ya ce barin wuta kadai ba zai dakile ayyukan masu kaifin kishin addini da sauran kungiyoyin da ke da alaka da al-Qa'ida a Siriya ba har sai an hura wuta ga kasashen yankin da ke taimaka musu a kan su daina mara musu baya. Bayanin na Walid al-Moallem na zuwa ne a dai-dai lokacin da Amirka da kawayenta ke ci gaba da yin ruwan bama-bamai a kan yankunan da 'yan IS suke a Siriyan, inda rahotanni daga masu rajin kare hakkin dan Adam ke nuni da cewa dakarun da Amirka ke wa jagora, sun kai hari a kan wani rumbun hatsi tare da hallaka fararen hula.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu