Soja sun karyata zargin fyade a Sudan
November 9, 2014Talla
Wannan karyata zargi dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da dakarun soja suka hana masu aikin wanzar da zaman lafiya isa yankin Tabit da ke arewacin Dafur, lokacin da suka kudiri aniyar zuwa yankin dan gudanar da bincike kan zargin aikata fyade ga manyan mata da'yan mata a yankin.
Kanal Al-Sawarmy Khaled Saad da ke magana da yawun sojan kasar ya fadi ga wani taron manema labarai cewa batun yi wa mata da yawa fyade a sudan abu ne dake zama sabo a garesu.
Wasu dai kafafan yada labarai na cikin gida ne dai suka bada rahotannin cewa wasu sojoji da suka yi batan dabo a karshen watan Oktoba sun shiga garin na Tabit inda suka yiwa manyan mata da 'yan mata 200 fyade.