Sojan Turkiya sun samu mafaka a Jamus
May 9, 2017Jamus ta bada mafakar siyasa ga wasu dakarun sojan kasar Turkiya da iyalansu kamar yadda kafafan yada labarai na nan Jamus suka bayyana a ranar Litinin. Wannan dai na zuwa ne bayan da take kara tsami a dangantaka tsakanin kasashen biyu da ke zama kawaye a Kungiyar tsaro ta NATO.
Babu dai karin bayani daga ma'aikatar harkokin cikin gidan na Jamus sai dai kafafan yada labarai irinsu jaridar Sueddeutsche Zeitung da kafafan watsa labarai na WDR da NDR sun ce mahukuntan na Jamus sun bada tabbaci na bada mafakar siyasa ga wadannan jami'ai na Turkiya.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan na Jamus dai a watan da ya gabata ta bayyana cewa ta karbi takardun neman mafakar siyasa daga wasu 'yan kasar ta Turkiya da ke da fasfo na diplomasiya 262 sai dai ba ta fayyace ko sojan kasar da ke aiki da Kungiyar tsaro ta NATO nawa ne ke cikin masu neman mafakar ba. Tun dai juyin mulkin da ya gaza nasara a watan Yuli na 2016, manyan jami'ai 414 da suka hadar da jami'an diplomasiya da sojoji da alkalai sun nemi mafakar siyasa a Jamus.