Sojin Iraki sun shiga Mosul
November 2, 2016Rahotanni daga kasar Iraki na cewa dakaran gwamnatin kasar sun yi nasarar kutsawa cikin birnin Mosul a kokarinsu na neman kwoto birnin daga hannun Kungiyar IS. Shugaban kwamnadan sojojin kasar ta Iraki Janar Taleb Cheghati al-Kenani ne ya sanar da hakan inda ya ce dakaransu sun samu shiga birnin na Mosul ta daga Gabashinsa. Kuma yanzu haka sun ja daga a unguwar Judaidat Al- Mufti inda daga nan suke shirin shiga gadan-gadan cikin yaki kwato birnin baki dayansa.
Sai dai masana harakokin yaki na gani kwato birnin na Mosul ba zai kasance cikin sauki ba ganin cewa akwai mayakan Kungiyar ta IS dubu uku zuwa dubu biyar wadanda za su yi kokarin yin turjiya ta kare birnin wanda a cikinsa ne jagoran nasu Abou Bakr al-Baghadadi ya ayyana kansa khalifan sabuwar daular Muslunci bayan kwace birnin daga hannun dakaran gwamnatin Iraki a shekara ta 2014.